Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

"Yan Siyasa Su Rungumi Zaman Lafiya"-Farfesa Galadanci


Babbar Sallah a masallacin tarayya
Babbar Sallah a masallacin tarayya

Yawancin mazauna Abuja babban birnin tarayyar Nigeria sun yi sallar layya a masallacin kasa dake birnin inda limamin masallacin ya kira 'yan siyasa su nemi zaman lafiyar kasa a zaben dake zuwa badi

Bayan sallar idi,limamin babban masallacin kasa dake Abuja Farfesa Shehu Sa'id Galadanci, ya kira 'yan siyasa da su yi takatsantsan saboda babban zabe da za'a gudanar shekara mai zuwa.

Farfesa Galadanci ya roki 'yan siyasa da su yi kokarin ilmantar da magoya bayansu tare da wayar da musu da kai kan neman zaman lafiya ta hanyar kaucewa hatsaniya.

Shi ma ministan babban birnin tarayya Muhammad Musa Bello, ya bayyana ranar sallah a matsayin babbar rana dake da matukar mahimmancin gaske. Ya nemi shugabanni a duk matakai su ji tsoron Allah.

Wadansi mazauna birnin na Abuja suna da ra'ayi mabanbanta gameda irin hali da sallar ta same su a ciki. Yayinda Haji Hafsat Sha'aibu ke yiwa Allah godiya saboda koshin lafiya da mallakar abun yin abun sallar, wani cewa ya yi mutane da yawa na cikin wani irin halin rayuwa, saboda shi kansa layyar hadaka ya yi domin rashin kudi.

Akwai wanda ya yiwa Allah godiya kasancewa ya na da rai amma bai samu ya yi yanka ba sanadiyar fama da rashin kudi.

Yanzu dai mata da yara suna kai da kawowa a wuraren shakatawa a ci gaba da bukukuwan sallar.

A saurari rahoton Hassan Maina Kaina

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:19 0:00

Facebook Forum

Zaben 2023

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG