Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarkin Musulmi Ya Yi Kiran A Rungumi Zaman Lafiya


Jawabin Sarkin Musulmi Alhaji Mohamammad Sa'ad Abubakar ya karkata ne akan bukatar yan Najeriya su rungumi zaman lafiya.

Kamar yadda aka saba a kowacce Sallah, sarkin Musulmi kan yi jawabi da kuma kira ga al'umma, akan haka ne Alhaji mohammed Sa'ad Abubakar, ya bukaci 'yan siyasa da su kauce ma siyasar ko a mutu ko ayi rai, muddin ana son ci gaban demokradiya a kasar Najeriya.

Ya kara da cewa siyasa ana yinta ne domin al'umma, yace idan babu zaman lafiya to babu shuwagabanci.

Yayi kira ga matasa da su kaurace ma bangar siyasa, kuma ya kara da cewa duk dan siyasar da ya ba matasa kwayoyi suyi bangar siyasa, suce ya saka 'ya'yansa gaba su sa biyo bayansu.

Wakilinmu Murtala Faruk Sanyinna Ya aiko mana da wannan rahoton.

please wait

No media source currently available

0:00 0:21:54 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG