Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Litinin Za a Yankewa Ram Rahim Hukuncin Laifin Fyade a Indiya


A Indiya masu zanga-zanga magoya bayan Ram Rahim Singh, sun fara tafiya gidajensu domin kawo karshen jan daga da sojoji.

Dubban magoya bayan wani babban malamin addini a kasar Indiya da aka samu da laifin fyade sun fara barin shelkwatarsa dake Sirsa, a arewacin kasar India yau Lahadi, abin da ya kawo karshen jan daga da suka yi da sojoji.

Mabiya Ram Rahim Singh, wanda yake kiran kansa Waliyi, kuma shugaban wata kungiyar addini, sun yi biyayya da kiran da hukumomi suka yi masu, da cewa su watse, bayan gudanar da wani kazamin bore da ya yi sanadin mutuwar mutane talatin da shida, kimanin dari uku kuma suka ji rauni.

Ranar litinin za a yankewa Singh hukumci kan laifin fyaden da aka sameshi da aikatawa, jami’ai kuma suna fargaban magoya bayansa zasu sake tada kayar baya idan suka ci gaba da zama a shelkwatar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG