Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lochte ya ci zinari a gasar Olympic, Phelps kuma ya zo na hudu


Bukin bude wasan na 'Olympic'

Dan wasan ninkayan Amurka Ryan Lochte ya yi galaba bisa babban abokin karawarsa Michael Phelps

Dan wasan ninkayan Amurka Ryan Lochte ya yi galaba bisa babban abokin karawarsa Michael Phelps da sauran ‘yan gasar iyo a jiya Asabar, inda ya ci gasar iyon mita 400 a wasannin Olympic din da ake yi a birnin London a wannan lokacin.

Thiago Pereira na kasar Brazil ne ya zama na biyu, bayan ya dan wuce dan kasar Japan Kosuke Hagino, wanda ya ci tagulla.

Phelps, wanda ya yi ta bin baya a akasarin lokacin gasar, ya zo na hudu, bayan sama da dakikoki hudu da isar wanda ya zo na dayan. Wannan dais hi ne karo na farko tun bayan wasannin 2000 da Phelps ya kasa cin koda ma tagulla a wasan Olympic.

A gasar gudu da keke na maza kuma, dan kasar Kazakhstan Vinokourov ya ci zinari, wanda al’amarin ya kawo cikas ga tsammanin da aka yi cewa Burtaniya za ta ci gasar ta tseren kilomita 250.

A gasar basirar seti da harbe-harbe, Amurka ta sadudar da Koriya ta Kudu inda ta haura matakin gasar cin zinari da kasar Italiya. Daga bisani dai kasar Italiya ce ta ci zinarin, bayan da ta doge Amurka da maki guda a gwaji na karshe.

A gasar judo na maza masu nauyin kasa da kilogram 60, dan kasar Rasha Arsen Galstyan ya ba wasu gwanaye biyu mamaki, ciki har da dan kasar Uzbekistan Rishod Sobirov da ya taba zama zaran duniya har sau biyu.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG