Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Lukaku Ya Nemi Afuwar Tuchel, Magoya Bayan Chelsea


Lukaku a hannun hagu (AP)

“Ya kamata a ce na fito na bayyana sakona ta yadda za a fi saurin fahimta," In ji Lukaku.

Dan wasan Chelsea Romelu Lukaku ya ba magoya bayan kungiyar, mai horar da su Thomas Tuchel da sauran abokan wasanda hakuri bisa wasu kalamai da ya yi da bai musu dadi ba.

Cikin wata hira da aka yi da shi makonni uku da suka gabat, Lukaka ya bayyana cewa “ba ya jin dadin” zama a kungiyar karkashin jagorancin mai horar da su Tuchel.

Ya kuma nuna cewa yana da muradin komawa kungiyarsa ta Inter Milan a nan gaba.

Wadannan kalamai ba su yi wa Tuchel da magoya bayan kungiyar da sauran abokan wasansa dadi ba, lamarin da ya sa aka ajiye shi a benci a wasan da Chelsea ta yi da Liverpool wanda aka tashi 2-2.

Sai dai ya koma atisaye a ranar Talata zai kuma buga gasar EFL da Chelsea za ta buga da Tottenham a ranar Laraba.

“Ya kamata a ce na fito na bayyana sakona ta yadda za a fi saurin fahimta, saboda hirar ta ban-kwana ce ga magoya bayan Inter Milan.” Lukaka ya ce, kamar yadda AP ya ruwaito.

“Na fahimci dalilin fushin magoyan Chelsea, amma yanzu ya rage a gare ni na nuna himmata 100 bisa 100.” In ji Lukaku.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG