Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikatan Lafiya a Brazil Sun Kai Shugaba Bolsonaro Kotun ICC


Shugaban Brazil, Jair Bolsonaro
Shugaban Brazil, Jair Bolsonaro

Ma’aikatan kiwon lafiya a kasar Brazil sun bukaci kotun hukunta manyan laifuka ta kasa-da-kasa da ta binciki gwamnatin shugaban kasar.

Suna son a binciki gwamnatin shugaba Jair Bolsonaro akan laifukan cin zarafin dan adam, da kuma yadda yake tunkarar annobar coronavirus.

An mika koken dake dauke da bayanan sheda daga kungiyoyin da ke wakiltar ma’aikatan kiwon lafiya sama da miliyan daya ga kotun dake Hague.

Kungiyoyin na zargin gwamnatin Bolsonaro da nuna halin ko-in-kula wajen fuskantar barkewar cutar COVID 19, wanda da ya sanya rayukan jami’an kiwon lafiya da kwararru da ma al’umma baki daya cikin hatsari.

Akwai rashin jituwa tsakanin Bolsonaro sauran gwamnonin jihoyin kasar inda yake kin amincewa da takaita zirga-zirga domin dakile yaduwar cutar ta coronavirus ciki har da dokar hana fita.

Shugaba Jair Bolsonaro
Shugaba Jair Bolsonaro

Bolsonaro wanda a kwanan nan aka auna shi ya warke daga cutar ta coronavirus, bayan da ya kamu da cutar tsawon makwanni 3 yana jinya, ya yi ta nanata cewa saka dokar kullen ya na kassara tattalin arzikin kasar.

Kasar ta Brazil na da adadi mafi yawa na kamuwa da cutar COVID-19 a yankin Latin America, inda take da mutum miliyan 2.4 masu cutar kuma sama da dubu 87,000 suka mutu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG