Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma’aikatan Lafiya, Banki Sun Shiga Zanga Zanga a Myanmar


Masu zanga zanga a Myanmar ranar 13, ga watan 2021.

Tun bayan da aka fara zanga zanga a Myanmar kan juyin mulkin da sojoji suka yi, ma’aikatan lafiya sun bi sahun masu wannan bore wajen nuna adawarsu da matakin sojin.

Ma’aikatan na lafiya sun shiga yajin aiki, inda suka ce ba za su koma bakin aiki ba sai an mayar da shugabannin da aka zaba kan karagar mulki.

Hakazalika da yawa daga cikin kwararru a fannoni daban-daban na rayuwa, su ma sun bi sahu, inda ma’aikatan banki, malamai da injiniyoyi suka kauracewa wuraren ayyukansu.

Hakan na faruwa ne a yayin da sojojin Myanmar suka jingine wasu dokoki da suke hana jami’an tsaro su kama wadanda ake zargi ko a binciki gidajen mutane, idan babu iznin kotu, inda suka ba da umurnin a cafke fitattun masu goyon bayan zanga zangar adawa da juyin mulkin da aka yi.

Wasu jerin sanarwa da aka fitar a rana ta takwas da aka yi ana zanga zanga akan juyin mulkin na ranar daya ga watan Fabrairu da kuma kama shugaba Aung San Suu Kyi, su suka katse tsarin da kasar ke bi wajen bin tafarkin dimokradiyya da yake ta taga-taga tun bayan da aka koma kansa a shekakar 2011.

Wannan juyin mulki ya haifar da bore a titunan kasar, wanda rabon da a ga irin tun bayan sama da shekara goma, wanda har ila yau kasashen yammacin duniya suke Allah wadai da shi, inda har Amurka ta ayyana takunkumi akan manyan sojojin kasar yayin da sauran kasashe kin shirin nasu matakai akan kasar.

XS
SM
MD
LG