Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma’aikatar Ilimin Amurka Na Shirin Korar Ma’aikata 1,300


Ma'aikatar Ilimin Amurka
Ma'aikatar Ilimin Amurka

Jami’an Ma’aikatar sun sanar da matakin a ranar Talata, inda suka tayar da ayar tambaya kan yadda hukumar za ta ci gaba da gudanar da ayyukan da ta saba gudanarwa.

Ma’aikatar Ilimi ta Amurka na shirin korar ma’aikatanta fiye da 1,300 a wani bangare na kokarin rage rabin ma’aikatan ma’aikatar, wani abu da ake ganin sharar fage ne ga shirin shugaba Donald Trump na rufe hukumar.

Jami’an Ma’aikatar sun sanar da matakin a ranar Talata, inda suka tayar da ayar tambaya kan yadda hukumar za ta ci gaba da gudanar da ayyukan da ta saba gudanarwa.

Gwamnatin Trump ta kasance tana son ta rage yawan ma’aikatan hukumar ta hanyar yi musu tayin biyan ajiye aiki da kuma korar ma’aikatan da ke mataki na gwaji.

Bayan korar ta ranar Talata, Ma’aikatan hukumar ta ilimin za su zama kusan rabin yadda suke a baya na 4,100, a cewar hukumar.

Korar da aka yi wani bangare ne na umarnin ragewa yawan ma’aikata da Trump ya bayar yayin da yake yunkurin rage adadin ma’aikatan gwamnatin tarayya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG