Ma’aikatar lafiya ta tarayyar Najeriya ta ce zata kafa wata cibiya ta bincike da harhada magunguna da itatuwa da kuma tsirrai don magance cututtukan dake shafar alumma.
Daraktar dake kula da sashen magungunan gargajiya a ma’aikatar lafiya ta kasa, Hajiya Zainab Sharif, ta ce ganin yadda magungunan da ake samu daga itatuwa ke yin tasiri wajen magance cututtuka yasa tun farko aka sa batun a kundin darussan da ake koyawa a wasu jami’o’in Najeriya.
Shugaban wata cibiyar hada magunguna daga tsirrai a garin Keffi dake jihar Nassarawa, Dakta Adamu Ahmad Bunkau, ya ce a binciken da ya yi, ya gano cewa kowacce cuta tana da magani.
Shi ma Evangelist Joel Hamajulde Gashaka, dake addu’o’i da jinyar masu tabin hankali a garin Lafia, jihar Nasarawa ya ce bada horo da hukumar lafiya za ta yi a fannin hada magungunan, zai taimaka musu wajen samun karin ilimi a aikinsu.
Ga karin bayani cikin sauti.
Za ku iya son wannan ma
-
Yuni 05, 2023
Yajin Aiki: Tinubu Zai Kafa Kwamiti Don Duba Bukatun NLC
-
Yuni 04, 2023
Kaura Ya Zama Shugaban Kungiyar Gwamnonin PDP
-
Yuni 03, 2023
Ana Ci Gaba Da Takaddama Kan Cire Tallafin Man Fetur
Facebook Forum