Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikatan Ceto Na Kokarin Cimma Mutanen da Girgizar Kasa Ta Rutsa Dasu cikin Tsaunuka


Girgizar kasa a Afghanistan

Ma'aikatan ceto na faman cimma wadanda girgizar kasa ta rufe cikin tsaunuka tsakanin Afghanisatan da Pakistan

Ma’aikatan ceto na ta faman kokarin cimma wasu wurare cikin tsaunuka a Pakistan da Afghanistan da girgizar kasa mai karfin 7 da digo 5 na ma’aunin rikta ta auku a kasasehn.

Ta hallaka akalla mutane 360 da raunata fiye da 2,200 a tsakanin kasashen biyu. Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani ya fada a shafinsa na Twitter a jiya Talata cewa, yawan mamatan kasarsa ya karu zuwa 115.

Sai kuma wadanda suka jikkata da suka kai akalla mutane 518 a yankuna 9 na kasar ta Afghanistan. Mutuwar ta hada da wasu ‘yan mata dalibai su 12 da aka tattake su garin gudu.

Lokacin da suke kokarin ficewa daga gine-ginen da ke layin Faduwa a Lardin Takhar. Masu aikin agaji sun ce taimakawa dukkan wuraren da girgizar kasar ta shafa zai dauki lokaci.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG