Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta ce mayakan kungiyar IS ne keda alhakin kai harin da aka kai Kudu maso Yammacin jamhuriyar Nijar, wanda ya kashe sojojin Amurka hudu. Haka kuma sabbin bayanan da aka samu sun nuna cewa wasu ‘yan kauyen da aka kai harin sun taka rawa.
A jiya Laraba wata mai magana da yawun ma’aikaar Pentagon, Lt Col. Michelle Baldanza, ta fadawa Muryar Amurka cewa mayakan IS sune suka kai harin kwantan baunar kan sojojin Amurka da Nijar, ranar 4 ga watan Oktoba, wanda kuma ya kashe sojojin Nijar hudu.
Dakarun Amurka na musamman da ake kira Green Berets, sun kammmala wani taro da wasu shugabannin kauyen kenan, suna takawa zuwa motocinsu aka kai musu hari, a cewar wani jami’in Amurka wanda yayi magana da Muryar Amurka kan batun amma ya nemi a sakaye sunansa ganin cewa har yanzu ba a kammala binciken ba.
Ma’aikatar tsaron Nijar ta tabbatar da faruwar musayar wuta a kusa da kauyen Tongo-Tongo dake yankin Tillaberi. Sojojin Nijar takwas sun raunata a harin, haka kuma sojojin Amurka biyu suma sun sami rauni, kuma an daukesu zuwa kasar Jamus domin kula da lafiyarsu.
Facebook Forum