Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikatan Tsaron Amurka Tace ISIS Na Iya Ta'adanci Koina A Duniya


Ashton Carter, sakataren tsaron Amurka

Jami'an Amurka suna gargadin cewa karfin kungiyar ISIS na iya janyo ayyukan ta'addanci a fadin duniya, ciki har da Amurka, ba tareda wata mu'amala tsakanin kungiyar da wadanda zasu gudanar da danyen aikin ba.

"Muna cikin wani sabon babi na ta'addanci a fadin duniya, inji mukaddashin sakataren ma'aikatar tsaron cikin gida Alejandaro Mayorkas, a bayani da yayi a gaban wani kwamitin majalisar dokokin Amukar jiya Alhamis.

"Saboda yanayin irin wadan nan hare hare da suka samo sarsala daga farfagandar ISIS, yana da wuya jami'an aikin leken asiri da dana tsaro, su gano su gabannin su kai hare haren, kuma hakan yana iya aukuwa ba tareda an sani ba," inji sakatare Mayorkas.

Dan majalisar dattijai Tom Carper na jam'iyyar Democrat, yace ya amince da matsayar hukumar tsaron cikin gidan, ya bada misali da harin da aka kai a San Barnerdino jihar California, da maharan suka halaka mutane 14.

Daga Iraqi kuma, rahotanni sun ce mazauna birnin Fallujah wadanda suke arcewa daga zazzafar bata kashin da ake yi tsakanin mayakan sakan ISIS da dakarun Iraqi, suna cikin halin "dimuwa," saboda tsananin amon wuta, da kuma matsanancin 'yunwa da suka shiga.

Shugaba Joe Biden ya zama Shugaban Amurka na 46

Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris

BIDIYO: Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:51 0:00

An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris

BIDIYO: An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46
please wait

No media source currently available

0:00 1:45:22 0:00
XS
SM
MD
LG