Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawan Amurka Zata Ci Gaba da Binciken Zargin Cewa Rasha Ta Yiwa Zaben Amurka Shishshigi


Wasu 'yan majalisar dattawan Amurka
Wasu 'yan majalisar dattawan Amurka

Majalisar Dattawn Amurka zata cigaba da binciken zargin da ake yiwa Rasha cewa ta yiwa zaben Amurka na shekarar 2016 shishshigi da nufin karkata tunanen masu zabe

Kwamitin tattara bayanan sirri na Majalisar Dattawan Amurka ya bayyana cewa zai ci gaba da bincikensa don gano ko kwamitin kamfen din shugaban kasa Donald Trump ya hada kai da kasar Rasha wajen sauya alkiblar zaben Amurka na shekarar 2016, yayin da ke gargadin cewa katsalandan din Rashar zai iya ci gaba ya kuma zamo barazana ga zabbukka masu zuwa.

Shugaban kwamitin,Richard Burr ‘dan jam’iyyar Republican daga jihar North Carolina, yace, “Har yanzu maganar katsalandan din zaben tana nan.”

Duk da yake basu fitar da wasu bayanai ba kan alakar mukarraban shugaba Trump da binciken ba, shugabannin kwamitin Richard Burr da Mark Warner, sunce sunga ya dace su fito su bayyana abin da suka gano izuwa yanzu a binciken da suke gudanarwa.

Yawancin manyan jami’an harkokin tsaron kasa na Trump sun amince da sakamakon da kwamitin tattara bayanan sirri na Majalisar Dattawan ya samu, na cewa Rasha ta yi katsalandan a zaben shekarar da ta gabata, ta kuma taimakawa Trump a zaben. Sai kuma shugaba Trump bai amince ba.

Facebook Forum

Zaben 2023

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG