Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mabiya Shi'a Sun Yi Gangami a Abuja


Sheikh Ibrahim Yaqub El-Zakzaky shugaban kungiyar Shiya da har yanzu yake tsare

Yau mabiya Shi'a da Shaikh Ibrahim El Zakzaki ke jagoranta sun fito suna neman a sako shugabansu kafin a tursasasu daukan makamai

Yau dubban mabiya shi'a daga sassa daban daban suka fantsama a titunan Abuja babban birnin Najeriya suna neman a sako masu jagoransu Shaikh Ibrahim El Zakzaky wanda har yanzu hukumomin Najeriya ke tsare dashi.

Suna mai cewa yanzu ashirye suke su dauki kowane irin mataki domin su ga an sakomasu jagoransu tare da cewa "abun ya isa haka. Kura ta kai bango"

Suna cewa "ba wai bamu san inda zamu samo makamai ba ne. Mun san hanyoyin kasuwar bayan fage da zamu iya samo makamai amma wannan ba ita ce manufarmu ba. Mu ba 'yan Boko Haram ba ne. Amma dai a sani cewa kura ta kai bango".

Abdullahi Zango ne yayi jawabi jim kadan bayan sun kammala gangamin.

Gungun 'yan shiya da suka shiga Abuja daga jihohin Najeriya sun dinga daga kwalaye dake cewa a sako masu jagoransu.

Ali Babba daya daga cikin wadanda suka shiga gangamin yana mai cewa bukatarsu ita ce adalci. "Ba wai muna bukatan wani abu ba ne..Kama Malam da aka yi, aka raunatashi, an yi zaton ma an kasheshi, an harbi iyalinshi, an kashe mashi 'ya'ya guda shida, aka kashe mashi albajirai fiye da dubu daya, wannan shi ne kololuwan zaluncin da aka taba gani. a wannan kasa".

Ali ya cigaba da cewa Malam Zakzaky bai yiwa mutanen Najeriya laifi ba ko wani bangare na kasar laifi ba. "Bawan Allah ne wanda yake son ganin hadewar kasar amma sai gashi azzalumai wadanda suke cutar da kasar su ne 'yan lelenta".

A cewarsa shi da aka zalunta a gidansa aka je aka kamashi aka kulle. Ya hada da cewa "cigaba da tsare Malam yanzu ba karamin zalunci ba ne".

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:19 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG