Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Madugun Adawa A Uganda Yace Zasu Cigaba da Gwagwarmaya


Shugaban 'Yan adawa Dr. Kizza Besigye s

Shugaban jam’iyar hamayya na kasar Uganda Dr Kizza Besigye na jam’iyar FDC ko "Forum for Democratic Change" ya yi kira ga magoya bayansa kada suyi kasa a guiwa a fafatukar inganta kasar.

Cibiyar dillancin labarai ta kasar Uganda ta ruwaito Besigye yana shaidawa manema labarai cewa, suna fafatuka ne na kwato kasarsu kuma, babu gudu babu ja da baya sai sun cimma wannan burin.

An kama Besigye wanda ya zo na biyu a zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Fabrairu, ana zarginsa da cin amanar kasa bayanda ya ayyana kansa shugaban kasa. An bada belinshi jiya Talata. Yayin bada belinsa, alkali ya bukaci shugaban hamayyar ya daina aikata abinda zai kawo tashin hankali ya kuma tabbatar da zaman lafiya tsakanin al’umma har zuwa lokacin da za a kammala bincike.

George Kanyeihamba, tsohon alkalin kotun kolin kasar Uganda yace, yayinda alkalin yake da ikon gindiya shadarorin bada belin, musamman a zargin da ya shafi cin amanar kasa, al’ummar kasar Uganda suna mamakin irin sharudan da suke gani sun tauye ‘yancin Besigye.

Bidiyo

Mijin Aljana A Kano: Shin Dama Aljanu Na Da ATM’ Na Kudi?
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:04 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG