Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tana Kasa Tana Dabo A Kasar Uganda


Zaben shugaban kasa da aka yi ranar 18 ga watan Fabarairun wannan shekarar a Kasar Uganda, mai cike da takaddama ya sa babbar jam’iyyar adawa ta Forum for Democratic Change (FDC) a takaice sanar da cewa ita ma zata rantsar da dan takararta Kizza Basigye gobe Alhamis in Allah ya kaimu, rana daya da za’a rantsar da shugaba Yoweri Museveni wani sabon wa’adin mulki, Musaveni dai shine ke shugabancin kasar tun shekarar aluf dari tara da tamanin da shidda.

Hukumar zaben Uganda ta ce shugaba Museveni ne ya lashe zaben da aka yi da kuri’u 61 cikin dari amma Basigye dan takarar jam’iyyar FDC, ya hakikance akan cewa lallai shine ya lashe zaben wanda ya sami kuri’u 52 cikin dari. Basigye dai ya na ta fafutikar nuna rashin cancantar shugaba Musaveni a matsayin shugaban kasa.

Gwamnatin Uganda ta hana kafafen yada labaran kasar daukar duk wani abu da jam’iyyar FDC za ta yi.

Matar Basigye, Winnie Byanyima ta kira muryar Amurka daga Kigali a Rwanda, inda take halartar wani taron koli akan tattalin arziki, ta fadi cewar an baza sojoji ko’ina a Kampala, babban birnin Uganda. Ta kara da cewa an girke jami’an tsaro a gidajen mukarraban jam’iyyar ta adawa, ciki har da gidan Basigye.

XS
SM
MD
LG