Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Maduro Ya Zargi Wasu Amurkawa Da Kai Wa Venezuela Hari


Shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro
Shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro

Shugaban Venezuela Nicolas Maduro ya ce wasu Amurkawa biyu na daga cikin sojojin haya ‘yan ta’adda da suka nemi kai wani farmaki da bai yi nasara ba a kasarsa a farkon makon nan.

Maduro ya nuna hoton paspo din mutanen ta talbijin wadanda ya yi ikirarin cewa na Airan Berry da Luke Denman ne, wadanda ke cikin mutum 13 da aka kama a wani farmaki da aka kai ranar Lahadin da ta gabata wanda bai yi nasara ba.

Maduro ya zargi Berry da Denman da aiki tare da Jordan Goudreau, wani tsohon sojin Amurka wanda ke da wata cibiyar harkokin tsaro mai zaman kanta a Florida da ake kira Silverco USA.

Berry da Denman tsofaffin sojojin Amurka na musamman ne, wadanda kuma ake kira Green Bereis.

Jami’an sojin Venezuela sun ce an kama maharan ne a lokacin da suka yi yunkurin su shiga birnin La Guaira ta jirgin ruwa daga makwabciyar kasar Columbia.

An dai kashe mutum 8 a farmakin wanda bai yi nasara ba.

A ranar Litinin din da ta gabata an nuna hotunan wasu maza kwance a kasa da hannuwansu a daure ta baya, a talabijin a Venezuela.

A wani bidiyo da aka saki a kafofin sada zumunci, Goudreau ya amince cewa shi ne ya kitsa harin.

Sai dai Shugaban Amurka Donald Trump ya ce babu hannun Amurka a wannan harin da bai yi nasara ba.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG