Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Maduro Ya Zargi 'Yan adawa Da Yunkurin Kifar Da Gwamnatinsa


Yadda aka yi artabu tsakanin masu zanga zanga da dakarun kasar Venezuela

Wasu hotunan bidiyo sun nuna wata motar jami’an tsaro tana bi ta kan masu zanga zangar, wadanda su kuma suka yi ta jefa duwatsu akan dakarun kasar.

Gwamnatin Venezuela ta yi ikrarin cewa akwai wata makarkashiya da aka kitsa ta kifar da ita, inda rahotanni ke cewa shugaban ‘yan adawa da Amurka ke marawa baya Juan Guaido, ya sha alwashin "ba gudu ba ja da baya” a kokarin da yake yi na ganin an kifar da gwamnatin Nicolas Maduro.

Dubban masu zanga zanga sun bazama akan titi Caracas, babban birnin kasar, inda aka rika jin tashin bindiga yayin da dakarun da ke goyon bayan Shugaba Maduro suka rika fetsa ruwa ga masu boren.

Wasu hotunan bidiyo sun nuna wata motar jami’an tsaro tana bi ta kan masu zanga zangar, wadanda su kuma suka yi ta jefa duwatsu akan dakarun kasar.

A wani sakon Twitter, Guaido ya rubuta cewa, “a yau zaratan dakaru masu kishin kasa, masu jarumtaka da ke goyon bayan kundin tsarin mulkin kasa, sun amsa kiranmu.”

Amma shugaba Maduro ya mayar da martani a shafin na Twitter, “na yi magana da dukkan kwamandojin yankunan kasar nan, wandanda suka tabbatar mana da mubaya’arsu ga daukacin al’umar kasar nan.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG