Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Magidanta Na Fargabar Farashin Kayan Masarufi Gabanin Ramadana


Yan Kasuwa Na Auna Shinkafa

A lokacin da ake gab da fara azumin watan Ramadan, ‘yan kasuwa da magidanta na fatan ganin farashin kaya ya sauka don samun sauki ga masu saye da sayarwa.

Sau tari magidanta na shiga zullumi da fargaba musamman idan lokacin bukukuwa na tunkarowa, kamar bikin sallah ko zuwan watan Ramadana ko kuma bikin kirsimeti, sakamakon yadda kayan masarufi ke tashin goron zabi.

Hakan yasa a dukkan lokacin da watan Ramadana ya karato, mutane kanyi tanadi abinda ya shafi cimaka da sauran abubuwan bukatu tun kafin lokacin.

Kayan Marmari Abinci
Kayan Marmari Abinci

Muryar Amurka ta ziyarci kasuwar FCDA dake Babban birnin tarayya Abuja inda 'yan kasuwar suka shaida cewa tashin bai taka kara ya karya ba kuma suna fatan a kara samun saukin farashin kayan.

Akan bukaci kayan marmari da dabino a lokacin azumi hakan yasa tuntubi Malam sabo Mai dabino don ji ta bakin sa, inda ya bayyana cewa kayayyakin sunyi tsada.

Anfi danganta faruwar wannan al’amari ga ‘yan kasuwa, kan tsauwalawa kayan masarufi da kayan cimaka da sauran abubuwan bukata.

Sai dai Asifu dake kasuwar FCDA yace yadda suka samo kayan haka suke kasawa.

A bana ma magidanta asun koka game da yadda kayan masarufi ke kara kudi, suna masu kira ga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su duba al'amarin

Saidai wasu na dora alhakin akan gwamnati data kasa tsaida kyakykyawan farashi wadda yake da ka’ida.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwace bindigogi sama da 500

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Shugaban NDLEA a Najeriya, Janar Buba Marwa

Dalilin Da Ya Sa Muke Bin Diddigin Dukiyar DCP Abba Kyari - Buba Marwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Gwamna Matawalle

Dalilan Da Suka Sa Muka Sayi Motoci Ga Sarakuna A Zamfara - Gwamna Matawalle
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG