Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Magungunan Cutar HIV Yana Iya Taimakon Marasa HIV


Wani yana rike da kwayar maganin cutar HIV
Sakamakon wadansu gwaje-gwaje guda biyu a Afrika ya nuna cewa idan mutane da ba su da cutar HIV suka sha magungunan kashe kaifin cutar HIV, yana iya hana su kama cutar ko sun yi cudanya da wadanda suke dauke da cutar ta hanayar da yana yiwuwa su kamu.

An gudanar da bincike ne a kan wadansu ma’aurata daga shekara ta dubu biyu da takwas zuwa dubu biyu da goma a Kenya da Uganda. Daya daga cikin ma’auratan bashi da cutar daya kuma yana da ita.

Binciken ya nuna an sami raguwar hadarin kamuwa da cutar kanjamau tsakanin kashi 67% zuwa 75% na wadanda suka sha maganin kashe kaifin kwayar cutar HIV, idan aka kwatanta da wadanda basu sha maganin ba.

Sai dai ba a sami irin wannan kariyar a bincike na uku da aka gudanar tsakanin mata daga kasashen Kenya da Afrika ta Kudu da Tanzaniya ba.

Binciken da aka buga a mujallar aikin magani da ake New England Journal of Medicine ya bayyana cewa, shan magani ba zai iya maye gurbin amfani da kwararon roba ba.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG