Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Magungunan zazazabin cizon sauro na jabu sun cika kasuwannin kasashen Afrika


Wani yana duban maganin da ya siya

Bincike na nuni da cewa, galibin magungunan da ake sayarwa a kemis-kemis na zazzabin cizon sauro a nahiyar Afrika jabu ne.

Bincike na nuni da cewa, galibin magungunan da ake sayarwa a kemis-kemis na zazzabin cizon sauro a nahiyar Afrika jabu ne.

Bisa ga rahoton, an shafe sama da shekaru goma ana sayar da magungunan zazzabin cizon sauro na jabu a kasashen kudu maso gabashin Asiya da kuma kasashen nahiyar Afrika dake yankin Hamada.

Rahoton yana nuni da cewa, yawan magungunan jabu da kasuwanni da kuma dadewa da jama’a suka yi suna amfani da su a duhunce yana kawo cikas a yunkurin yaki da zazzabin cizon sauro da kuma shawo kanshi.

Kwarrarru sun bayyana cewa, amfani da magungunan zazzabin cizon sauro na jabu yana iya hallaka mutum, sabili bashi da wani sanadarin yaki da cutar ko kashe kaifinta.

Bisa ga cewar kwararrun, magungunan da basu da karfin da zasu iya kashe kaifin cutar zazzabin cizon sauro suna da matsala ainun sabili da suna haddasa jikin mutum yaki jin magani nan gaba. Abinda zai sa cutar malariya ta sha karfin mutum ta kuma maida magungunan da yake sha wofi.

Kasashen nahiyar Afrika da dama suna da hukumomin dake sa ido a kan magungunan da ake sayarwa a kasuwanni, sai dai sau da dama, cin hanci da rashawa yana hana hukumomin gudanar da aikinsu yadda ya kamata abinda ke jefa al’ummar kasar cikin hadarin sayen magungunan jabu a duhunce.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG