Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahaifan Otto Warmbier Sun Ce Ya Cimma Burinsa Kafin Ya Mutu


Otto Warmbier

Shugaban Amurka Donald Trump ya yiwa iyayen Otto Warmbier ta'aziya wadanda suka ce dansu ya cimma burinsa kafin ya bar duniya

Mahaifan Otto Warmbier, dalibin kwalejin nan ba’amurke da ya mutu ranar Litinin bayan da aka tsare shi a Korea ta Arewa har na tsawon kusan shekara daya da rabi, sun fada a wata sanarwa cewa ya cimma burinsa na dawowa gida, kuma ya samu natsuwa jim kadan kafin ya mutu.

Shugaban Amurka Donald Trump a jiya Litinin ya aikewa da iyalansa sakon ta’aziyya, yana mai cewa “abu mafi alhini shine iyaye su rasa dansu yayin da yake ganiyar kuruciyarsa.”

Trump ya kuma kira gwamnatin Korea ta arewa a matsayin “mara imani” inda ya kara da cewa wannan lamari ya kara mai kaimin mayar da hankali wajen ganin irin wannan abin alhini bai sake aukuwa a hanun gwamnatocin da ba su maida ran bil’adama a matsayin komai ba.

Jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Nikki Haley, ta fada cewa mutuwar Warmbier za ta ci gaba da tunatar da su kan “muguwar gwamnati irin ta Korea ta Arewa.”

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG