Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahaifin Michael Da Janet Jackson Ya Rasu


Joe Jackson

Joseph Jackson, mahaifin fitattun mawakan nan na Amurka da ake kira Jackson family, ya rasu, bisa ga wata majiyar da take kusa da iyalin.

Majiyar da ta nemi a sayata sabili da rashin izinin yin Magana a fili kan rasuwar tasa, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Associated Press yau Laraba cewa, ya rasu, sai dai bata yi wani Karin haske a kai ba. Joseph Jackson, ya rasu yana da shekaru tamanin da tara a duniya.

Mamacin wanda shine mahaifin Michael Jackson, da Janet Jackson, da kuma fitattun ‘yan’uwansu, ya fitar da iyalinsa daga talauci a birnin Gary, jihar Indiana, ya kafa wata zuriya ta fitattun mawaka.

Yayanshi maza biyar-Michel da Jermaine, da Marlon da Tito da kuma Jackie sun yi fice a shekara ta dubu da dari tara da sittin da tara lokacin da suka fara waka da suna Jackson five.

Miliyoyin mutane sun saurari wakokin iyalin na Jackson, yayinda Michael Jackson ya kasance daya daga cikin fitattun mawaka a tarihi kafin rasuwarsa a shekara ta dubu biyu da tara.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG