Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahaifin Oprah Winfrey Ya Mutu


Oprah Winfrey a wani lokaci a can baya a Jami'ar Havard
Oprah Winfrey a wani lokaci a can baya a Jami'ar Havard

Ya rasu ne a birnin Nashville na jihar Tennessee da ke Amurka a ranar Juma’a kamar yadda ta sanar.

Vernon Winfrey, mahaifin fitacciyar mai gabatar da shirye-shirye kuma kusa a fagen kafafen yada labarai a Amurka, Oprah Winfrey, ya rasu.

Shekarun Winfrey 89.

Oprah ce ta sanar da rasuwar mahaifin nata a shafinta na Instagram kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.

Ya rasu ne a birnin Nashville da ke jihar Tennessee a ranar Juma’a kamar yadda ta sanar.

“Tare da iyalansa a zagaye da shi akan gandonsa, na shaida yadda mutumin da ya yi dawainiya da rayuwata, ya yi numfashinsa na karshe.

“Mun ji yadda salama ta shiga dakin a lokacin da ya cika.” Oprah ta rubuta a shafin nata na Instagram.

Ba a dai bayyan shirye-shiryen yadda za a gudanar da jana’izarsa ba.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG