Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahaifiyar Alan Waka Ta Rasu


Alan Waka da mahaifiyarsa marigayiya Hajiya Bilkisu Sharif Adam (Instagram/ Alan Paka)

“Allah ya sa Aljanna makomarki Hajiya, Allah ya jaddada rahama.” Alan Waka ya rubuta a shafinsa na Instagram.

Mahaifiyar shahararren mawakin Hausa, Aminu Ladan Abubakar da aka fi sani da Alan Waka ta rasu.

Hajiya Bilkisu Sharif Adam ta rasu a ranar Litinin tana da shekara 70, kamar yadda Alan Waka ya bayyana a shafinsa na sada zumunta.

“Allah ya sa Aljanna makomarki Hajiya, Allah ya jaddada rahama.” Alan Waka ya rubuta a shafinsa na Instagram.

“Ta rasu ta bar ‘ya’ya guda biyu da jikoki ashirin da biyar. Aminu Ladan Abubakar da Khadija Ladan Abubakar su ne ‘ya’yan da ta bari. Allah ya jikan ta da rahamna ya sa Aljanna makoma.” Mawakin ya kara da cewa a wani rubuta na daban da ya wallafa.

Tuni jarumai da furdusoshin Kannywood suka yi ta mika ta'aziyyarsu abokin sana'arsu.

“Allah ya jikan ta da rahama.” In ji Yakubu Mohammed.

“Allah ya jikan ta da Rahama. Ameen summa Ameen.” Teema Yola ta rubuta.

“Allah ya jikan ta, Allah ya sada ta da rahamar manzon Allah S.A.W.” Abdulamart mai Kwashewa ya ce.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG