Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahaifiyar Jaruma Maryam Booth Ta Rasu


Marigayiya Haj. Zainab Booth, hagu da 'yarta Maryam Booth, dama (Instagram/ Ali Nuhu/Maryam Booth)
Marigayiya Haj. Zainab Booth, hagu da 'yarta Maryam Booth, dama (Instagram/ Ali Nuhu/Maryam Booth)

A ‘yan watannin baya, Maryam Booth ta wallafa a shafinta na Instagram cewa a taya mahafiyarta da addu’a saboda za a yi mata aiki.

Hajiya Zainab Musa Booth, mahaifiya ga jarumar masana’antar Kannywood da Nollywood Maryam Booth ta rasu.

Marigayiya Zainab, wacce ita ma tsohuwar jaruma ce da ke fitowa a matsayin uwa a fina-finan na Kannywood, ta rasu ne a daren Alhamis za kuma a yi jana’izarta a ranar Juma’a.

“Allah ya yi wa Hajiya Zainab Musa Booth rasuwa, gobe za a yi jana’iza a gidanta da ke kallon Premeire Hospital a Court Road da karfe takwas. Allah ya jikanta da rahama” In ji Jarumi Ali Nuhu, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Tuni jaruman masa’antar ta Kannywood maza da mata suka yi ta mika sakonnin ta’aziyyarsu ga iyalan marigayiyar.

“Allah ya gafarta miki da rahamarsa, ameen” Ramadan Booth ya rubuta a shafinsa na Instagram.

“Muna mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalanta. Allah ya yafe mata kurakurenta.” In ji jaruma Daso.

“Allah ya jikan mommy mama zee, rayu kenan. Allah ya sa idan ta mu ta zo mu cika da imani ya rabbi.” In ji Rashida Mai Sa’a.

A ‘yan watannin baya, Maryam Booth ta wallafa a shafinta na Instagram cewa a taya mahafiyarta da addu’a saboda za a yi mata aiki.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG