Iyayen matashiyar nan Leah Sharibu wacce mayakan Boko Haram suka yi garkuwa da ita, sun yi kira ga hukumomin Najeriya da su cika alkawarin da suka dauka na ceto ‘yarsu.
A wani taron manema labarai da ta kira a Abuja, Rebecca Sharibu, mahaifiyar Leah, ta ja hankalin mahukuntan kasar da su cika alkawarin da suka yi mata cewa za a kwato mata ‘yarta.
“Sati daya nan gaba, za ta cika shekara daya, shi ya sa na zo gabanku da gaban gwamnati….(ta fashe da kuka) Ina rokon gwamnati ta taimake ni kar ta manta alkawarin da ta yi min.” Inji Rebecca Sharibu cikin hawaye.
Kungiyoyin kare hakkin bil Adama da shugabannin addini, na daga cikin masu yin kira da a saki Leah.
A ranar 19 ga watan nan na Fabrairu, Leah za ta cika shekara guda a hannun mayakan na Boko Haram.
Taron manema labaran da Rebecca ta kira na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta jitajitar cewa mai yiwuwa matashiyar ta rasu.
Saurari cikakken rahoton Medina Dauda:
Za ku iya son wannan ma
-
Janairu 30, 2023
ZABEN 2023: Matakin Abuja, Babban Birnin Tarayya
-
Janairu 30, 2023
Shugaba Muhammadu Buhari a Jihar Kano
-
Janairu 29, 2023
CBN Ya Kara Kwana 10 Kan Wa’adin Daina Karbar Tsofaffin Kudi