Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahara Biyar Da Wani Soja Sun Mutu a Somaliya


Shugaban Somaliya Mohammed Abdullahi Farmajo
Shugaban Somaliya Mohammed Abdullahi Farmajo

Ga dukkan alamu dai mahara sun sha alwashin sa kasar Somaliya gaba. Ko a jiya Asabar sai da su ka yi yinkurin sake yin kashe-kashe a wannan galabaitacciyar kasar, to sai dai Allah bai ba su nasara ba. A maimakon haka ma, an hallaka dukkanninsu biyar; su kuwa soja daya ne kawai su ka hallakar.

Mutane a kalla shida ne su ka mutu -- ciki har da mahara biyar -- a wasu hare hare biyu na jiya Asabar daura da Fadar Shugaban kasa a Mogadishu, babban birnin kasar Somaliya a cewar Shaidu.

A cewar wadanda al'amarin ya auku a gabansu, wata mota wadda ta sheko a guje ne ta tarwatse a wani wurin duba ababen hawa daura da lambun shakatawar nan na Peace Garden, wanda wuri ne na gwamnati, daga nan kuma sai aka shiga musayar wuta tsakain jami'an tsaro da 'yan bindigar.

Rahotanni na nuna cewa jami'an tsaro sun yi matukar fafatawa da 'yan bindigar har sai da su ka murkushe su.

Rahotannin da aka faru samu na nuna cewa duka-duka mutane shida ne su ka mutu: wato da wani sojan gwamnati da kuma 'yan bindigar su biyar.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG