Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahara Sun Kai Farmaki A Madagali


wadansu kauyuka da kungiyar Boko Haram ta kaiwa hari
wadansu kauyuka da kungiyar Boko Haram ta kaiwa hari

Rahotanni daga jihar Adamawa arewa maso gabashin Najeriya na cewa, wadansu maharan Boko Haram sun kai farmaki a yankin Madagali dake daura da dajin Sambisa inda suka yi kone –kone da harbe harbe.

Kamar yadda al’umman yankin suka tabbatar,mayakan na Boko Haram sun kai farmaki ne ta yankin kauyen Yahza dake tsakanin jihohin biyu inda suka yi barna masu dinbin yawa, ciki har da gidaje da kuma amfanin gona.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, yace yanzu haka al’ummomin wadannan yankuna na cikin wani mawuyacin hali na zaman dar-dar da kuma fargaba.

Koda yake kawo yanzu hukumomin tsaro basu yi Karin haske ba kan lamarin, amma kuma dan Majalisar Wakilai dake wakiltar yankin Madagali da Michika, Hon Adamu Kamale,ya tabbatar da wannan sabon harin ya kuma koka game da sabbin hare haren da ake kaiwa yankunan, ya kuma bukaci da a kara yawan dakaru a garuruwan.

Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdul’aziz.

An kai hari a Madagali-2:33"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:33 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG