Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Maharan Boko Haram Sun Kashe Mutane Hudu A Kamaru


Jami'an tsaro sun kwashe baraguzan mutanen da 'yan Boko Haram suka hallaka da bam a Jakana cikin Kamaru

Wasu maharan kungiyar Boko Haram sun kai harin kunar bakin wake a wani wurin cin abinci a garin Jakana dake jihar Arewa Mai Nisa cikin kasar Kamaru

Maharan Boko Haram sun kai wani sabon hari a garin Jakana ta jihar Arewa Mai Nisa inda suka kashe mutane guda hudu a cikin gidan cin abinci.

Wani dan kato da gora da ya dago maharan ya rungumi daya daga cikin maharan wanda shi kuma nan take ya tayar da bam din dake kinisa. Dan kato da goran da dan kunar bakin waken nan take suka sheka lahira. Wadanda suka jikata kuma suna asibiti inda ake kula dasu.

Daya daga cikin wadanda suka jikata
Daya daga cikin wadanda suka jikata

Wani dan garin yace basu ji dadin abun da ya faru ba saboda yawan afka masu da 'yan Boko Haram su keyi. Yace daya daga cikin 'yan kato da gora da aka sa a garin saboda 'yan ta'adan ya gano mutumin amma kafin ya kamashi sai bam ya tashi. Mutane hudu da suka hada da dan ta'adan ne suka mutu kana wasu da dama suka ji munanan raunuka.

Mutumin ya kira gwamnatin Kamaru da ta tashi tsaye ta taimaki yankin saboda yawan harin kunar bakin wake da ake kai masu. Gwamnan jihar ma ya ziyarci inda aka kai harin inda ya nuna bakin cikinsa da lamarin.

Ga rahoton Garba Lawal da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00

XS
SM
MD
LG