Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shahararren Dan Jarida Mahmoon Baba-Ahmed Ya Rasu


Mahmoon Baba-Ahmed

A yau ne 9 ga watan nan na Fabrairu, shahararen dan jaridar Mahmoon Baba Ahmed ya rasu a jihar Kaduna ta Najeriya,

Marigayi Mahmoon ya rasu yana dan shekaru 74 da haihuwa bayan fama da rashin lafiya. Ya bar mata daya da ‘yaya ‘ya’ya bakwai da kuma ‘yan uwansa da dama.

Daga cikin ‘yan uwan nasa har da Hakeem Baba-Ahmed, shugaban ma’aikatan ofishin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Bukola Saraki. An yi jana’izarsa a Masallacin sarki Musulmi Bello da ke Unguwar Sarki a Kaduna.

Kafin rasuwarsa, yayi aiki a gidan rediyon gwamnati, inda bayan ya yi ritaya ya koma kafafen yada labarai masu zaman kansu, kamar DITV mallakar zuri’arsu, da kuma tashar talbijin ta Liberty da ke Kaduna inda yake gabatar da shirye-shirye kamar su Tambihi da Dimukuradiyya.

Ko kafin ya bar duniya sai da ya rubuta sharhinsa da saba mai taken Muryar ‘Yanci da ya ke yi ana saka wa a tashar ta Liberty. Haka kuma yana rubuce-rubucen da ake makalawa a jaridu daban-daban na Najeriya na Hausa da Turanci.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG