Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai Bincike Na Musamman Ya Yiwa Atoni Janar din Amurka Tambayoyi


Jeff Sessions, Atoni Janar din Amurka kuma Ministan Shari'a
Jeff Sessions, Atoni Janar din Amurka kuma Ministan Shari'a

Wani kakakin Ma'aikatar Shari'ar Amurka ya tabbatar da cewa mai bincike na musamman akan zargin yin katsalandan da Rasha ta yi a zaben shekarar 2016 ya yiwa Jeff Sessions tambayoyi na wasu sa'o'i da dama.

A yau Talata, wani kakakin ma’aikatar shari’ar Amurka, ya ce, ofishin lauya na musamman, Robert Meuller, da aka nada domin binciken katsalandan din da ake zargin Rasha da yi a zaben Amurka na 2016, ya yi wa babban Attoney Janar din Amurkan, Jeff Session tambayoyi a makon da ya gabata, kan shishhigin da Rashan ta yi.

Jaridar New York Times ce ta ruwaito labarin a yau Talata, inda ta ce, Sessions ya fuskanci tambayoyi na tsawon sa’o’i, a ci gaba da binciken na Rashan.

An kuma yi wa Sessions tambayoyi, kan ko shugaba Trump ya nemi ya dakatar da binciken, tun bayan da ya hau mulki a watan Janairun bara.

Kakakin ma’aikatar shari’ar, Ian Prior, ya tabbatar wa Muryar Amurka cewa lallai an yi wa Sessions tambayoyi, amma, ya ki ya yi karin bayani.

Lauyan Sessions na kansa, Chuck Cooper, da kuma ofishin Mueller, duk sun ki su ce komai kan tambayoyin da aka wa Sessions din a lokacin da Muryar Amurk ta tuntube su.

Babban Attoney Janar din, shi ne jami’in gwamnmatin Trump na farko da aka yi wa tambayoyi, tun bayan da Meuller ya karbi binciken na Rasha a watan Mayun bara.

A daya bangaren kuma, Fadar shugaban Amurka ta White House, ta bayyana kwarin gwiwarta, kan Darektan hukumar binciken manyan laifuka ta FBI, Christopher Wray, wanda rahotanni suka bayyana cewa ya yi barazanar ajiye aikinsa, saboda matsalin lambar da shugaba Trump ya ke nuna mai, na sai ya kori mataimakinsa, Andrew McCabe.

Shafin yanar gizon yada labarai na Axios, ya wallafa cewa, Jeff Sessions, tare da umurnin Trump, ya matsa sai Wray ya kori McCabe, da wasu jami’an hukumar ta FBI da suka yi aiki tare da tsohon darektan hukumar, James Comey, bisa zargin cewa sun nuna bangarancin siyasa, yayin da suke gudanar da ayyukansu.

Facebook Forum

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG