Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai Shigar Da Kara A Kotun ICC Ya Nemi A Kama Shugaban Isra’ila Da Na Hamas


ICC - Karim Khan mai shigar da karar Netanyahu da Hamas
ICC - Karim Khan mai shigar da karar Netanyahu da Hamas

Babban mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifukan yaki ta duniya ya nemi a kamo shugabannin Isra’ila da Hamas a ranar Litinin, wadanda suka hada da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, kan irin matakan da suka dauka a yakin da suka kwashe watanni bakwai ana yi.

WASHINGTON. D. C. - Yayin da Netanyahu da ministan tsaronsa, Yoav Gallant, ba sa fuskantar kame cikin gaggawa, sanarwar da babban mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ya yi, wata alama ce ta alama da ta zurfafa warewar Isra'ila kan yakin Gaza.

Karim Khan
Karim Khan

Mai gabatar da kara na kotun, Karim Khan, ya zargi Netanyahu, Gallant, da shugabannin Hamas uku; Yehia Sinwar, Mohammed Deif da Ismail Haniyeh da aikata laifukan yaki da cin zarafin bil'adama a zirin Gaza da Isra'ila.

Benjamin Netanyahu
Benjamin Netanyahu

Netanyahu da sauran shugabannin Isra'ila sun yi Allah wadai da matakin da cewa abin kunya ne da kuma nuna wariya.

Shugaban Amurka Joe Biden ya kuma caccaki mai gabatar da kara tare da goyon bayan ‘yancin Isra’ila na kare kanta daga Hamas.

Biden, Netanyahu, ICC
Biden, Netanyahu, ICC

Kwamitin da ya kunshi alkalai uku ne za su yanke shawarar ko za su bayar da sammacin kama su da kuma ba da damar ci gaba da shari’ar, wanda alkalan sukan dauki watanni biyu kafin su yanke irin wannan hukunci.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG