Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai Yiwuwa Korea Ta Arewa Za Ta Koma Tattaunawa Da Amurka


Trump da Jong Un

Korea ta Arewa, ta amince ta koma teburin tattaunawa da Amurka kan batun makamin nukiliyanta, a cewar wani babban jami’in diflomasiyan kasar, kamar yadda kafofin yada labarai suka ruwaito.

A cewar mataimakin Ministan harkokin wajen Korea ta Arewa, Choe Son Hui, hukumomin Pyongyang da na Washington, sun amince su zauna a ranar biyar ga watan nan na Oktoba, sai dai ba a ambaci inda tattaunawar za ta wakana ba.

Amma a jawabinsa na farko da ya yi, tun bayan da ya bar gwamnatin Trump, tsohon mai ba da shawara kan harkokin tsaro, John Bolton ya nuna shakku kan yiwuwar samun maslaha a tsakanin Amurkan da Korea ta Arewa.

Sanarwar sake hawa teburin tattaunawa tsakanin kasashen biyu, na zuwa ne kusan watanni uku, bayan da Shugaba Trump da takwaran aikinsa Kim Jong Un, suka hadu a yankin nan mara soji da ya raba Koriyoyi biyu.

Duk da cewa bangarorin biyu sun amince su sake zama bayan wannan ganawa, Korea ta Arewa ta ki sake bayyana ranar da za a sake zama.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG