Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisa Ta Amince Da Karin Kasafin Kudi Naira Biliyan 895 Da Buhari Ya Gabatar


Sanata Ahmed Lawan
Sanata Ahmed Lawan

Majalisar Dokokin Najeriya ta amince da kasafin kudi na Naira biliyan 895 da Shugaban kasa Mohammadu Buhari ya mika mata makonni biyu da suka wuce.

Kasafin na kunshe na da kudaden kashi 80% cikin 100 da za a inganta harkokin tsaro da kuma samo magungunan cutar coronavirus da sauran kashi 20% cikin 100.

Majalisar ta amince da wanan kwarya-kwaryar kasafin ne da kari domin a cewan Sanata Barau Jibrin wanda shi ne Shugaban Kwamitin kula da harkokin kasafin kudi na Majalisar Dattawa, an yi kyakyawan nazari kafin a dauki wannan matakin.

Barau Jibrin ya ce an ware ma dukkan bangarorin tsaro daga sojojin kasa, da na sama da na ruwa, da bangaren ‘yan sanda duk an yi masu karin kudade da za su kawo masu sauki wajen gudanar da aiyukan su.

To ko bangaren zartarwa sun fadi inda za a samo wadanan kudaden? Tambayar kenan da muka yi wa Sanata Barau wanda ya ce sun fadi asusu-asusu daban-daban da kuma inda za a samo kudaden da za a hada kan su wuri guda domin yin aikin.

Sai dai ga Mai nazari a al'amuran yau da kullum kuma kwararre a harkokin tsaro Dokta Yahuza Ahmed Getso ya yi tsokaci akan batun yana cewa an dade ana ruwa kasa tana shanyewa domin yana ganin jami'an tsaro sun gaji da korafin rashin kayan aiki kuma ai an dade ana ware masu kudade tun shekaru 6 da wannan Gwamnatin ta kafu amma ba a bin diddigin yadda ake sarrafa kudaden.

Amma a lokacin da ya ke jawabi akan kasafin kudin da muhimmancin sa ga kasa musamman a kan sha'anin tsaro Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan, ya bada tabbacin majalisa za ta sa ido sosai domin ta ga an yi amfani da kudaden yadda ya kamata.

Saurari rahoto cikin sauti daga Medina Dauda:

Majalisa Ta Amince Da Karin Kasafin Kudi Naira Biliyan 895 Da Buhari Ya Gabatar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:28 0:00


Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG