Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisa Ta Jajirce Sai Hamid Ali Ya Bayyana Sanye Da Kayan Sarki


Shugaban Hukumar Kwastan KanarHamidu Ali (Rtd)
Shugaban Hukumar Kwastan KanarHamidu Ali (Rtd)

Yau Shugaban Hukumar Kwastan Kanar Hamidu Ali mai ritaya ya bayyana a gaban Majalisar Dattawan Najeriya bisa ga alkawarin da ya yi cewa yau Alhamis din nan zai iya bayyana maimakon jiya.

Sai dai ga alama har yanzu tsuguno bai kare ba, domin an bashi umurnin ya sake bayyana a wani mako sanye da kayan sarki, saboda kin saka kayan da ya yi a yau.

Majalisar dokokin ta Najeriya ta kwashe makwanni ta na kai ruwa rana tare da shugaban na hukumar kwastam kan bayyana a gabanta ba tare da sa kayan sarkin ba.

Hakan ya sa wasu suke ganin dalilin ke nan da har ya sa suka bar shi ya kwashe mintina 55 ba'a bar shi ya ce komai ba.

Shi dai Ali ya tsaya tsayin daka cewa rashin sa kayan sarkin ko kuma uniform a turance, ba ya hana shi gudanar da ayyukansa.

Wani kuduri da Sanata George Sekibo ya kawo kan kundin tsarin mulki da ya ce dole ne duk dan kasa ya mutunta kundin da mutunta hukumominta.

Wannan kudurin da Sanata Sekibo ya gabatar, ya sa mataimakin shugaban Majalisar Ike Ekwerenmadu da ya jagoranci zamanta ya yi wa 'yan majalisar tambayar ko sun amince Hamid Ali ya sake dawowa a mako mai zuwa sanye da kayan sarki.

"Wa ya amince cewa shugaban hukumar Kwastan ya dawo ranar Laraba mako mai zuwa da karfe goma na safe cikin kayan sarkin mukaminsa da duk lambobin da kwantrola yake sawa?" Ekwerenmadu ya tambaya.

Dukkanin 'yan majalisar dai sun amince da cewa shugaban na kwastam ya bayyana a mako mai zuwa kuma sanye da kayan na sarki.

Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00

Facebook Forum

Zaben 2023

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG