Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisa Ta Yi Watsi Da Irin Yarjajjeniyar Da May Ta Cimma Ta Barin EU


Firaminista Theresa May
Firaminista Theresa May

Kamar yadda aka hango, Majalisar Dokokin Burtaniya ta kada kuri'ar rashin amincewa da irin yarjajjeniyar da Firaminista Theresa May ta cimma ta ficewa daga EU.

Firaministar Burtaniya Theresa May za ta fuskanci yiwuwar kada ma ta kuri’ar rashin amincewa a Majalisa a yau dinnan Laraba, bayan da ‘yan Majalisar Dokokin Burtaniya su ka kada kuri’ar rashin amincewa da tsarinta na ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai (EU).

Shugaban babbar jam’iyyar adawa ta Labor Party Jeremy Corbyn, ya bayyana cewa tuni ma ya gabatar da kudurin kada kuri’ar rashin amincewa da gwamnatinta nan da nan bayan abin da ya faru jiya Talata.

Idan aka kada kuri’ar rashin amincewa da May, Burtaniya za ta gudanar da babban zabe. To amma akasarin masu lura da al’amuran yau da kullum na ganin May za ta kai labari, kuma gashi ma jam’iyyar Northern Ireland marar rinjaye da May ta dogara ga ita ta ce za ta goyi bayan gwamnatin May.

Kuri’ar ta jiya Talata ita ce bijirewa mafi girma da wata gwamnati mai ci ta taba gani, inda ‘yan Majalisar Dokoki – ciki har da ‘yan jam’iyyar su May ta masu ra’ayin rikau da ke Majalisar su 100 da ke ma ta tawaye - su ka ki amincewa da irin yarjajjeniyar da ta cimma na ficewa daga kubngiyar EU.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG