Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Donald Trump Ya Zauna Da 'Yan Majalisa


Donald Trump
Donald Trump

'Yan majalisar dokokin Amurka sun bayyana ra'ayoyi kishiyoyin juna a kan jawabin da shugaban na Amurka Donald Trump yayi a zaman hadin guiwa na majalisun dokokin biyu, game da halin da kasa take ciki.

Dan majalisar wakilai daga jam'iyyar Republican Ryan Costello, ya kira jawabin na shugaba Trump a matsayin na ci gaba, domin ko ya bayyana abubuwan da ake bukata a cikin gida, misali batun inganta samar da ababen more rayuwa, da harkokin shige da fice.

Mr. Costello ya ce majalisar dokoki na bukatar daga yanzu ta yi amfani da sati mai zuwa, kai har ma watanni, domin ganin ta fadada wadannan kudurori na shugaba Trump.

Shi kuwa dan majalisar dattijai daga jam'iyyar Democrat, Chris Coon, yace yayi fatar ganin shugaba Trump ya gabatar da jawabin dake kumshe da burin sassa biyun za su yi aiki tare, kuma yayi kwakkwaran bayanin yadda za a inganta abubuwan more rayuwa. Tare da karfafa muradun Amurka a duk fadin duniya da kuma tinkarar matsalar Koriya ta Arewa, yace shugaban yayi haka a wasu sassa, a wasu kuma bai yi ba.

Shi ko dan majalisar wakilai dan jam'iyyar Republican, Brian Fitzpatrick, yace a ganinsa shugaba Trump yayi nasarar gabatar da jawabi wanda ya karfafa aiki tare.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG