Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bukatar Trump Ta Biya


Kakakin Majalisa Paul Ryan Bayan Zabe
Kakakin Majalisa Paul Ryan Bayan Zabe

Shugaban Amurka Donald Trump, ya samu nasarar kafa doka akan haraji, nasarar ta biyo bayan zaben da 'yan majalisar dokoki suka yi akan batun kuma masu rinjaye suka amince.

Majalisar dokokin Amurka, ta kada kuri’a jiya Talata akan yiwa tsarin harajin kasar garambawul, abinda ya sanya shugaba Donald Trump, da ‘yan majalisa daga jam’iyyarsa ta Republican, samun gagarumar nasarar yin doka da kuma cika alkawarin yakin neman zaben da suka yiwa jama’a amma da kyar.

Duka ‘yan majalisar jam’iyyar Republican, su 51 sun kada kuri’ar goyon bayan rage haraji da yin dokokin aiki, yayinda ‘yan jam'iyar Democrats, su 48 duk suka jefa kuri’ar kin amincewa da kudurin.

“Yau muna cikin wani muhimmin yanayi na canji akan tsarin harajin kasar mu cikin shekaru 30 kenan, a cewar shugaban kwamitin kasafin kudi a majalissar dattijai Mike Enzi, dan jam’iyyar Republican, mai wakiltar Wyoming. Ya kara da cewa wannan abin tarihi ne.”

Shi kuma dan kwamitin harkokin kudi na majalisar dattijai Ron Wyden, mai wakiltar Oregon cewa yayi, “yau ‘yan jam’iyyar Republican, sun juyawa masu matsakaicin karfi baya a hukumance”. Ya kuma ce ba za a manta da wannan canjin da aka samu akan haraji ba.

Dokar harajin yanzu ta rage haraji akan kamfanoni na din-din-din, ta kuma rage haraji akan ma’aikata dake karbar albashi na wani dan lokaci, ta kuma takaita yawan harajin da ake ragewa wasu, bayan haka bashin Amurka, zai karu da dala triliyan 1 nan da shekara 10.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG