Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Biritaniya Na Iya Hana Kasar Shiga Rikicin Siriya


Sakataren harkokin wajen Ingila William Hague.

Ta yiwuwa Frayim Ministan Biritaniya ba zai samu yadda yake so ba daga majalisar kasarsa na farma kasar Siriya game da zargin ta yi anfani da makamai masu guba.

Yayin da Frayim Ministan Biritaniya ya kirawo 'yan majalisar kasar daga hutun bazara da suke yi domin su yi muhawara dangane da irin martanin da kasar ya kamata ta mayarwa Siriya kan zargin ta yi anfani da makamai masu guba, kawunan 'yan majalisar ya rabu.

Kodayake Frayim Ministan Biritaniya ya yi barazanar farma Siriya babu tabbas 'yan majalisar kasar zasu amince idan Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya bai bada izinin yin hakan ba. Sai dai Sakataren Harkokin Wajen Biritaniya William Hague ya ce idan Majalisar Dinkin Duniya bata bada izini ba to fa wajibi ne kasar Biritaniya da kawayenta su mayar ma Siriya martani. Ya ce zamu cigaba da tattaunawar da muke yi a New York domin a cimma yarjejeniya domin a samu matsaya daya. To amma bujirewar kasashen China da Rasha ka iya kawo rashin samun cimmma yarjejeniya.

Kalamun Mr. William Hague sun kawo rudu a majalisar. Sun nemi karin haske bisa ga abun da Frayim Minista David Cameron ya kirasu su zo yi. Su na son su sani ko yana shirin daukan matakan soji ne a kan kasar Siriya. Shugaban jam'iyyar adawa ya ce babban hadari ne a dauki matakan soji ba tare da amincewar Kwamitin Sulhu ba.Ya ce ba za'a dorawa majalisarsu alhakin daukan matakan soja ba sai idan Majalisar Dinikn Duniya ta tsayar da kudirin yin hakan.

Mutane basu manta da abun da ya faru shekaru goma da suka wuce ba dangane da Iraqi lokacin da aka bada rahotannin cewa Saddam Hussain nada makaman kare dangi. Daga baya an gano cewa rahotannin na bogi ne. Sabili da abun da ya faru baya 'yan majalisar suna taka tsantsan.

Mohammed Sani Dauda nada rahoto.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG