Accessibility links

Majalisar Dattawa: An Bar Bukola Da Lawan

  • Ibrahim Garba

Cikin Majalisar Dattawan Najeriya

Ga dukkan alamu jam'iyyar APC ta kai ga cimma jituwa kan rage yawan 'yan takarar nemar kujerar Shugaban Majalisar Dattawa

A yanzu kokuwar nemar kujerar Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya ana yinta ne tsakanin Sanata Ahmed Lawan daga Arewa maso gabas da kuma Bukola Saraki daga arewa ta tsakiya.

Hakan ya biyo bayan janyewar da wasu fitattun ‘yan takara irinsu Sanata George Akume da kuma bangaren Sanata Danjuma Goje.

Wakilinmu a Abuja Nasiru Adamu Elhekaya ya ruwaito wani magoyin bayan Sanata Bukola Saraki mai suna Sanata Dino Melaye na cewa sun a son dan takaran na su ya zama Shugaban Majalisa ne saboda ba wanda za a juya shi ne kamar waina ba.

Ya yi watsi da yiwuwar Sanata David Mark na jam’iyyar PDP ya amfana da rigimar da ‘yan APC ke yi, ya ce tuni ‘yan PDP da dama su ka bayyana goyon bayansu ga bangarensu.

Shi kuma Sanata Bukar Abba Ibrahim ya ce shi kuwa ya na goyon bayan Ahmed Lawan ne saboda kusan dansa ne a siyasnace kuma ya cancanta.

XS
SM
MD
LG