Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawa Na Dakon Sunayen Ministoci


To ko yaya marasa rinjaye ke kallon wanna batu

Yau Majalisar dattawa ta fara samanta ne cikin raha sabanin irin hatsaniyar da ya faru jiya.

Shugaban marasa rijaye tsohon Gwamnan jahar Akwa Ibom, ya ja hankalin majalisa ga cewa yau ne karshen wata Satumba,kuma ba’a kawo sunsyen minstici ba kamar yadda shugaba Muhammadu Buhari, ya yiwa al’umar kasa alkawari.

Shi kuma mataimakin shugaban masu rinjaye Bala Ibn Na Allah, cewa yayi wata Satumba, bai kare ba sai an kai karfe, 12, na dare.

To ko yaya marasa rinjaye ke kallon wanna batu Ben Bruce, dan jam’iyyar PDP, cewa yayi muna da labarin cewa shugaban kasa yana kan hanyarsa ta dawowa daga New York, ta kasar Amurka,mai yuwa shi ya sa ba’a samu sunayen ba kuma ai har yanzu muna ranar karshe ne a watan Satumba, yana iya kawowa.

Daya daga cikin mahimmam abubuwan da majalisar tayi a yau su hada da nada mukamin mai tsawatarwa wanda sanata Adeyeye daga shiyar kudu maso yamma ya samu mukamin.

Majalisar Tarayyar Najeriya - 3'12"
XS
SM
MD
LG