Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawa Ta Bukaci Buhari Ya Sallami Manyan Hafsoshin Sojin Kasar


Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari

Majalisar Dattawan Najeriya ta bukaci Shugaba Buhari ya sallami manyan hafsoshin tsaron saboda matsalar rashin tsaro da ke kara ta'azzara a kasar.

Majalisar ta yi kiran ne a zaman da ta yi a ranar Talata inda ta nemi a maye gurbin manyan jami'an tsaron kasar da masu sabbin dabaru kamar yadda kafofin yada labaran Najeriya suka ruwaito.

Kiran na zuwa ne bayan kisan gillar da aka yi wa wasu manoma 43 da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne a karamar hukumar Mafa a jihar Borno.

Wata sabuwar muhawara kuma da ta sake kunno kai ita ce ta neman a dauko dakarun haya, abin rahotanni suka ce gwamnan jihar Borno Prof. Babagana Umara Zullum ya goyi baya.

Daya daga cikin mambobin kwamitin dattawan na al’ummar arewa maso gabashin Najeriya Mallan Abba Kaka ya ce, abin takaici ne a ce a cikin shekaru 11 an kasa shawo kan matsalar tsaro.

Ya kara da cewa, ya kamata gwamnatin ta samar da sojan haya domin a ganinsa wannan kadai ita ce hanyar da za a kawo karshen ayyukan ta’addanci a kasar.

Wannan ba shi ne karon farko da 'yan majalisar dokokin Najeriya suke neman a sauke manyan hafsoshin ba, ko a watan Janairu majalisar dattawan ta yi makamancin wannan kira bayan da ta lura al'amuran tsaro na kara tabarbarewa a kasar.

Saurari Karin bayani cikin sauti a Rahoton Umar Farouk Musa:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

An Yi Jana'izar Manoma 43 Da Aka Yi Wa Yankan Rago a Borno
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:26 0:00

XS
SM
MD
LG