Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tawagar Shugaban Najeriya Ta Kai Ziyarar Jajanta Wa Jihar Borno


Jana'izar Manoma 43 Da Aka Yi Wa Yankar Rago a Borno

Shugaba Muhammadu Buhari ya tura wata tawaga karkashin jagorancin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Ahamed Lawan, don jajanta wa al'ummar jihar Borno kan kisan gillar da aka yi wa manoman shinkafa 43 a kauyen Zabarmari.

Tawagar da shugaban ya aika ta bayyana jimami tare da alhinin da shugaban kasa ya yi game da kisan gillar da aka yi wa manoman shinkafa 43. Haka kuma shugaban kasa ya baiwa rundunar tsaron kasar umarnin gudanar da bincike don gano mutanen dake da hannu a ta’asar.

Gwamnatin Najeriya ta dauki tsauraran matakan ganin abin da ya faru a kauyen Zabarmari bai sake faruwa a kasar ba, a cewar tawagar.

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya yi kira ne ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kara taimaka wa al’ummar Borno. Inda ya ce, a taron gwamnonin shiyyar arewa maso gabas da aka gudanar a jihar Adamawa, sun lura da cewa Naira Biliyan 45 ne kadai aka ware ga jihohin wanda hakan ba zai yi wani tasiri ba ga tsaron yankin.

Haka kuma gwamna Zulum ya bayyana kin amincewarsa da kafa kwamitin binciken cin zarafin da 'yan sanda suka yi a jihar, ganin cewa gwamnatin tarayya ba ta kafa wani kwamiti na ganin an binciki kashe-kashen da kungiyar Boko Haram ke yi ba.

Domin cikakken bayani saurari rahotan Haruna Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00

An Yi Jana'izar Manoma 43 Da Aka Yi Wa Yankan Rago a Borno
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:26 0:00
XS
SM
MD
LG