Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawa Ta Kalubalanci Obasanjo


Olusegun Obasanjo
Olusegun Obasanjo

Wani dan Majalisar dattawa a Najeriya, ya yi kira ga tsohon shugaban kasar, Olusegun Obasanjo, da ya ba da hujja tare da bayyasan sunyen wadanda ya zarga da yin sama da fadi da wasu kudaden da aka ware musu domin mazabunsu.

Tsohon shugaban Najeriya ya aike ne da wata budaddiyar wasika zuwa shugabannin majalisun kasar, inda ya zarge su da yin facaka da kudaden kasar da kuma rashin bin doka.

Obasanjon har ila yau, ya yi zargin cewa mafi yawan ‘yan majalisun ba su gina ofisoshin mazabun da suke wakilta ba, duk da cewa sun karbi kudaden da aka ware domin yin hakan, yana mai cewa hakan ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.

Sai dai yayin da yake maida martani dangane da wadannan zarge-zarge, shugaban Majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya ce majalisar ta shimfida wasu matakai domin gujewa aukuwar wata badakala da kudaden majalisar.

Saraki ya kara da cewa nan ba da jimawa ba majalisar za ta fitar da kasafin kudin ta ga jama’ar kasar.

Ana shi bangaren, Sanata Bukar Abba Ibrahim, ya ce wasikar ta Obasanjo alama ce da ke nuna cewa tsohon shugaban kasar ya zaku ya ga cewa ana ci gaba da damawa da shi a siyasar kasar.

XS
SM
MD
LG