Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawan Amurka Ta Tabbatar da Jeff Sessions A Matsayin Atoni-Janar


Jeff Sessions Atoni-Janar na Amurka

Jiya Laraba Majalisar Dattawan Amurka ta kada kuri'ar amincewa da mutumin da Shugaba Donald Trump ya gabatar don zama Attoni-Janar din Amurka, bayan sun shafe fiye da kwana guda ana ta zafaffar muhawara, har ma da wata sa'insa, wadda ta kai ga dakatar da wata fitacciyar 'yan Democrat daga gabatar da jawabi.

Kuri'un da aka kada, 52 akasin 47, sun sa Jeff Session, wanda wani dadadden dan jam'iyyar Republican ne daga jahar Alabama, ya zama babban jami'in tabbatar da bin doka a Amurka, kuma na 6 cikin jerin mutanen da aka tabbatar da nadin nasu a gwamnatin Trump.

"Wannan karramawa ce ta musamman," a cewar Session ga takwarorin aikinsa a jawabin bankwana da ya yi bayan kuri'ar. "Ina fata da kuma addu'a cewa zan iya ba da mara da kunya ganin irin yaddar da kuka nuna ma ni. Zan yi iya iyawata inga hakan ya faru."

Session, magoyin bayan Trump na farko-farkoa lokacin yakin neman zaben bara da aka yi cikin matukar hayaniya, ya yi alkawarin fifita doka bisa siyasa a matsayinsa na Attoni-Janar.

XS
SM
MD
LG