Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawan Amurka Za Ta Fara Zafaffiyar Muhawara Kan Bakin Haure


Shugaban Masu Rinjaye Mitch McConnell

Kamar yadda aka zata tun farko, ranar Litini za a fara wata zafaffiyar muhawara kan bakin haure a Majalisar Dattawan Amurka, ganin an warware batun dokar kasafin kudi na wuccin gadi.

Majalisar Dattawan Amurka na shirin fara wata shu’umar muhawara kan bakin haure daga ranar Litini. Muhawarar za ta kasance wata iriya, saboda za a fara ta ne ba tare da ainihin takardar kuduri ba.

Shugaban Masu rinjaye na Majalisar Dattawa Mitch McConnell ya ce za a bude muhawarar ce da wata takardar kudurin doka wadda babu batun bakin haure ciki. Daga baya sai ‘yan Majalisar su bukaci a yi gyara ma takardar.

A cewar McConnell gyarar da za a yi za ta tabbatar da adalci a yayin muhawarar.

‘Yan Majalisar za su tattauna kan kan makomar wasu matasan bakin haure da ke zama karkashin wani shirin da ke kare su daga kora mai suna DACA a takaice. Za kuma su tattauna kan batun gina Katanga akan iyakar Amurka da Mexico, da tsarin shigowa Amurka ta hanyar canki-canki, da tsarin shigowa Amurka ta hanyar gayyatar daga wani dangi da dai sauran batutuwa.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG