Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawan Najeriya ta Dakatar da Sanata Ali Ndume Na Tsawon Wata Shida


Senator Ali Ndume

Dazu dazun nan ne Majalisar Dattawan Najeriya ta dakatar da Sanata Muhammad Ali Ndume har na tsawon watanni shida daga majalisar.

Sanata Muhammad Ali Ndume mai wakiltar kudancin jihar Borno shi ne shugaban masu rinjaye tunda aka kafa wannan gwamnatin har zuwa watanni biyu da suka gabata lokacin da aka cire shi.

Dakatar da shi Sanatan yanzu ba zai rasa nasaba da batun Ibrahim Magu ba wanda Majalisar ta ki ta tabbatar masa da kujerar shugabancin EFCC, hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa, har sau biyu. Yanzu ma Majalisar ta ba gwamnati makonni biyu ta sallami Ibrahim Magun daga mukaminsa.

Zamu kawo maku karin bayani.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG