Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawan Najeriya ta Dauki Mataki Kan Halin da Jihar Rivers ke Ciki


Ginin majalisar dokokin Najeriya

Takaddamar dake tsakanin gwamnatin jihar Rivers da kwamishanan 'yansandan jihar ta hana samun zaman lafiya lamarin da majalisar dattawa ta ce ba zata bari ya cigaba ba.

Kusan watanni bakwai ke nan da ake kai ruwa rana a jihar Rivers tsakanin gwamnatin jihar da kwamishanan 'yansaandan jihar.

Yayin da majalisar dattawa ta tayar da maganar lamarin ya jawo hayaniya da tayar da jijiyar wuya. Hayaniyar ta kawo tsaiko a majalisar har na tsawo mintuna ashirin.

Kabiru Gaya wani dan majalisar ya yi karin haske kan lamarin da matakin da majalisar ta dauka. Ya ce wani sanato daga jihar Rivers ya kawo maganar yana cewa ga irin halin da jihar ke ciki. Ya ce maganar da majalisar ta yi watanni bakwai da suka wuce ya kamata su sake dubata. Ya ce sun yi magana kan lamarin kuma da dama ransu ya baci. Majalisar ta yadda lallai a dauki matakin da za'a yi gyara.

Tun da abun ya hada da kwamishanan 'yansandan jihar majalisar ta bukaci a kira masu babban sifeton 'yansanda na kasa gaba daya. Majalisar na son ya zo gabansu ya yi masu bayani dalla-dalla. Idan ya zo zai yi masu bayani ne a fili yadda duniya zata ji bayanansa zuwa garesu.

Dangane da wai gwamnati bata yin komi da shawarwarin da majalisar ke bata domin haka ko sifeton ya zo babu abun da zai canza sai Sanato Gaya ya ce na farko dai zasu kirashi su ji shi. Kuma babu wadanda shugaban kasa ya kamata ya mutunta irin 'yan majalisa domin su ne wakilan 'yan Najeriya. Ya ce su ne abokanan aikinsa. Su ne ya kamata idan sun ji abun da ba daidai ba kuma sun gaya masa ya dauka ya yi aiki da shi. Aikinsu shi ne bada shawara. Idan ya ki sai su jawo hankalinsa bisa ga abubuwan da suka fada masa. Ya ce yana ganin za'a kaiga wannan matsayin idan ba'a yi gyara ba.

Sanato Gaya ya kara da cewa idan da an dauki shawarar da suka bayar watakila da ba'a kaiga inda ake ba yau. Ya ce sun je jihar sun yi bincike kana sun shaidawa shugaban kasa cewa kwamishanan 'yansandan jihar nada laifi. Ya ce sun fitar da dalilai masu kwari kuma sun ce a cireshi. Sun bukaci shugaban 'yansanda ya canza masa wuri domin a samu zaman lafiya a jihar Rivers.

To yanzu sai a sa ido a ga ranar da sifeton 'yansandan zai bayyana gaban majalisar da abun da ka biyo baya.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG