Majalisar Dattawan Amurka ta dauki wani irin matakin da ba ta taba daukawa ba kan kasar Saudiyya, kawar Amurka ta kud-da-kud, bayan da ta amince da wani kuduri na kawo karshen goyon bayan da Amurka ke bai wa Masarautar Saudi wadda ke kai dauki a yakin basasar da ake yi a kasar Yemen. Majalisar ta kuma amince da wani kudurin, na yin Allah wadai da kashe dan jaridar saudiyya nan, mai jayayya da Masarautar kasar, Jamal Khashoggi.
Wadannan matakan biyu, sun zama tamkar kashedi ga daya daga cikin kawayen Amurka na kud-da-kud. Majalisar ta kuma nuna bacin ranta kan mace-mace, da azabar da jama’a ke gani a Yemen. Ta kuma dora laifin kisan dan jarida, Jamal Khashoggi akan, Yariman Saudi Mai Jiran Gado Mohammed bin Salman.
“Tuni ya kamata ma mu ce abin ya isa hakanan,” a cewar Sanata Patrick Leahy, dan jam'iyyar Democrat. Shi kuma Sanata Marco Rubio, dan jam'iyyar Republican ya ce, “Duk wanda ya san tasirin Yariman Saudiyya Mai Jiran Gado, ya san cewa babu yadda za a yi wasu jami’ai wajen 17, wadanda kuma na kusa ne da shi, su shiga jirgi su tafi wata kasa, su yiwa wani mutum kisan wulakanci, a Karamin ofishin Jakadanci, su jefar da gawarsa, su dawo – sannan wai ace bai sani ba.”
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 04, 2023
Amurka Ta Kakkabo Babban Balan-Balan Na Leken Asirin China
-
Janairu 25, 2023
Mawakiya Yar Najeriya Ta Yi Tarihi A Bikin Bada Lambar Yabo Na Oscar
-
Janairu 13, 2023
Lisa Marie Presley, Diyar Mawaki Elvis Ta Rasu
-
Janairu 11, 2023
Ana Tsaftace Yankunan Da Mahaukaciyar Guguwa Ta Ratsa A California
Facebook Forum